Kemistiri a Cikin Ayyukan Yau-da-Kullum - Chemistry in Everyday Activities

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kemistiri Cikin Ayyukan Yau-Da-Gobe (Chemistry In Everyday Activities)


Gabatarwa

Kemistiri, fanni ne mai faɗi da kuma rassa da dama waɗanda suka duƙufa wajen ganin sun samar da cigaban rayuwar ɗan'adam. A bisa wannan dalili ya kusan babu wani fanni na rayuwa da kemistiri bai gaurayu da shi ba.

A wannan darasi za mu ɗan leƙa wasu sassa na rayuwar yau-da-kullum mu ga irin gudunmawar da kemistiri ya bayar a ciki.

Kalli Wannan Bidiyon Domin Ƙarin Bayani

  1. Fannin Aikin Gona (Agriculture): A fannin aikin gona, kemistiri yana da matuƙar amfani. Ta hanyar sa ne ake samar da taki (synthetic fertilizer) da sauran sinadaran da suka yi matuƙar sauƙaƙawa tare kuma da haɓɓaka aikin gona. Misali, maganin fashin ciyawa (herbicide), maganin kashe ƙwarin gona (pesticide), da sauran su.
  2. Fannin Abinci (Food): Kemistirin abinci (food chemistry) yana bayar da gagarumar gudunmawa wajen samar da sinadaran da ke taimakawa wajen sarrafawa tare kuma da adana abinci ba tare da an yi hasararsa ba. Ana amfani da sinadarai wajen busar da abinci (dehydration), sandarar da shi (freezing) da sauransu domin adanawa. Haka nan kuma akwai sinadaran da ake amfani da su wajen samar da bitamin, maiƙo, kala, ɗanɗano, ƙamshi, da sauran su.
  3. Fannin Harhaɗa Magunguna (pharmaceutical): Ana aiki da kemistiri wajen harhaɗa magunguna wanɗanda kuma ake amfani da su wajen warkar da cututtuka.
  4. Fannin Masaƙu (textile): A wannan fanni kemistiri yana amfani wajen samar da sinadaran saƙa da kuma turin kayan da ake saƙawa kamar irin su yadi, atamfa da sauransu.
  5. Fannin Albarkatun Mai (Fuel): Ana amfani da kemistiri wajen haƙowa da kuma tace mai wanda yake a matsayin makamashi a matakai da dama.
  6. Tama da Ƙarafa (metallurgy): Ana amfani da kemistiri wajen gano sinadaran ƙarafa (metals), kamar irin su iron, copper, aluminium, da sauransu.
  7. Fannin Kayan Gini (synthetic materials): Ana amfani da kemistiri wajen samar da kayan gine-gine da suka haɗa da na rufi kamar kwanon rufi, tayil, siminti, da sauransu.
  8. Fannin Lafiya (healthcare): A fannin lafiya, kemistiri yana da gudunmawar da yake bayarwa kamawa tun daga harhaɗa magunguna da kuma sanin adadi, yanayi da kuma lokacin da za a yi amfani da su.
  9. Tsaftar Muhalli (environment): Kemistiri ya zurfafa bincike a fannin tsaftar muhalli, jiki, tufafi da kuma abinci. Shi ne ya gano irin sinadaran da za a yi amfani da su wajen kashe ƙwari (insecticide); sabulun waka da na wanki (soap and detergents); turaren ƙamsasa ɗaki, jiki da kuma tufafi (perfumes) da kuma mayukan wanke haƙora (toothpaste) da sauransu.
  10. Kimiyyar Binciken Laifuffuka (forensic science): Kemistiri ya samar da hanya da kuma kayan aikin da ake amfani da su wajen bankaɗo masu aikata laifuffuka tun daga kan ƙanana har zuwa manya kamar kisan kai.

Manazarta:


ACS Chemistry for Life (2020). Chemistry Careers. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.acs.org/content/acs/en/careers/college-to-career/chemistry-careers.html

AGCAS (2020). Chemistry. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.prospects.ac.uk/careers-advice/what-can-i-do-with-my-degree/chemistry

AGCAS (2020). Nuclear engineer. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.prospects.ac.uk/job-profiles/nuclear-engineer

Better Health (2017). Workplace safety - hazardous substances. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.betterhealth.vic.gov.au/health/healthyliving/workplace-safety-hazardous-substances

Cleveland Clinic (2018). Household Chemical Products and Their Health Risk An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://my.cleɓelandclinic.org/health/articles/11397-household-chemical-products-and-their-health-risk

Mendeley (2018). Top Ten Chemistry Jobs. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.mendeley.com/careers/article/top-10-chemistry-jobs/

Moore J.T (2020). Ten Great Careers in Chemistry. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.dummies.com/education/science/chemistry/ten-great-careers-in-chemistry

Tucker L. (2019). What Can You Do With a Chemistry Degree? An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.topuniversities.com/student-info/careers-advice/what-can-you-do-chemistry-degree

United States Department of Labor (2020). Chemical Hazards and Toɗic Substances. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.osha.gov/SLTC/hazardoustoxicsubstances/


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub